Shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewar kayan abincin da matasa suke wawashewa ba na gwamnati bane.

Hakan ya fito daga bakin mai magana da yawunsa Mallam Garba Shehu a tattaunawarsa ba BBC.
Ya ce kayan abincin masu kuɗi ne suka tattara don agazawa al umma don rage yunwa a tsakanin jama a sakamakon cutar Korona.

Ya ƙara da cewa abin takaici ne yadda wasu matasa suka ɓalle ɗakin ajiyar abincin a wasu jihohi kuma abin rashin jin daɗi ne.

Ya ce abincin ba tallafin gwamnati bane na ƴan kasuwa da manyan masu kuɗi ne.
Wasu matasa ne dai suka ɓaɓɓalle ɗakunan ajiyar abinci tare da wawashesu a wasu jihohin Najeriya kamar Pilato, Adamawa, Kaduna da sauransu.