Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya miƙa sunan Farfesa Mahmood Yakubu a matsayin shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC.

Hakan na ƙunshe a sanarwar da mai magana da yawunsa Femi Adesina ya fitar, ya ce shugaban ya miƙawa majalisar dattawa sunan Farfesa Mahmood don amincewa tare da tantanceshi aa matsayin shugaban hukumar karo na biyu.

Wannan dai shine karo na biyu da Farfesa Mahmood zai kasance shugaban hukumar bayan ya jagoranci zaɓen shugaban ƙasa da gwamnoni da ƴan majalisar wakilai da majalisar dattawa da majalisar dokokin jihohi a shekarar 2019.

Duk da kasancewarsa shugaban hukumar a yanzu, sai ya sake tsayuwa a gaban majalisar dattijai don tantancewa kafin a amince kamar yadda kundin taarin mulkin ƙasa ya tanadar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: