Shugaban rukunin gidajen gonar Nana Farms Nigeria LTD Alhaji Muhammad Aminu Adamu wanda aka fi sani da Abba Boss ya ce tsarin tafiyar DAMARKA NA HANNUNKA ba iya siyasa ya tsaya ba.

Hakan ya fito daga bakinsa  yayin da yake jawabi a kan muhimmancin dogaro da kai ga matasa maza lokacin da mujallar Matashiya ke bikin yaye matasa 200 da aka koyawa sana’a kyauta.

Ya ce ba lallai sai mutum ya dogara da aikin albashi ba, idan mutum ya koyi sana a ta fi masa domin zai iya bawa wani aikin yi.

Ya bada misali da cewar a baya lokacin yana aikin albashi, da kansa yake sakawa kansa kuɗin da zai ke ɗauka a wata, amma ya ajiye ya koma kiwon kaji wamda ya fara da guda ɗari kacal, kuma yanzu mutane da yawa ne suke ci a ƙarƙashinsa.

Abba Boss ya buƙaci matasan da suka koyi sana a Mujallar Matashiya da su riƙe sana ar hannu bibbiyu domin babu aikin da gwamnati za ta bayar a wannan lokaci.

Sannan ya taya murna daa bikin cika shekaru huɗu da kafuwar Mujallar Matashiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: