Connect with us

Labarai

Babu aikin da gwamnati zata bawa Matasan a Najeriya, Damarka na Hannunka – Abba Boss

Published

on

Shugaban rukunin gidajen gonar Nana Farms Nigeria LTD Alhaji Muhammad Aminu Adamu wanda aka fi sani da Abba Boss ya ce tsarin tafiyar DAMARKA NA HANNUNKA ba iya siyasa ya tsaya ba.

Hakan ya fito daga bakinsa  yayin da yake jawabi a kan muhimmancin dogaro da kai ga matasa maza lokacin da mujallar Matashiya ke bikin yaye matasa 200 da aka koyawa sana’a kyauta.

Ya ce ba lallai sai mutum ya dogara da aikin albashi ba, idan mutum ya koyi sana a ta fi masa domin zai iya bawa wani aikin yi.

Ya bada misali da cewar a baya lokacin yana aikin albashi, da kansa yake sakawa kansa kuɗin da zai ke ɗauka a wata, amma ya ajiye ya koma kiwon kaji wamda ya fara da guda ɗari kacal, kuma yanzu mutane da yawa ne suke ci a ƙarƙashinsa.

Abba Boss ya buƙaci matasan da suka koyi sana a Mujallar Matashiya da su riƙe sana ar hannu bibbiyu domin babu aikin da gwamnati za ta bayar a wannan lokaci.

Sannan ya taya murna daa bikin cika shekaru huɗu da kafuwar Mujallar Matashiya.

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

Kotu Ta Dakatar Da EFCC Daga Kama Tsohon Gwamnan Kogi Yahya Bello

Published

on

Babbar kotun jihar Kogi da ke zamanta a Lokoja ta dakatar da hukumar hana cin hanci da rashawa EFCC kamawa, tsarewa tare da gurfanar da tsohon gwamnan jihar Yahaya Bello.

 

Umarnin kotun wanda ta yanke a yau Laraba, ta hana hukumar kama tsohon gwamnan har said a izinin kotu.

 

Alƙalin kotun Justice I.A Jamil ne ya karanto hukuncin byan da hukumar ta matsa don ganin ta kama tsohon gwamnan.

 

Ana zargin tsohon gwamnan da yin sama da faɗi da wasu kuɗaɗen jihar a lokacin da ya na gwamna.

 

Kotun ta soke umarnin wata kotu a jihar da ta bai wa hukumar dammar kama tsohon gwamnan.

 

A yau Laraba ne hukumar ta kai sumame don kama tsohon gwamnan a gidansa da ke Abua, sai dai daga bisani ya tsallake kamun wanda aka tseratar da shi.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Continue Reading

Labarai

An Maida Masu Bukata Ta Musamman Baya A Cikin Gwamnatin Tarayya

Published

on

Ƙungiyar masu buƙata ta musamman ta arewacin Najeriya ta koka a kan yadda ake sake mayar da su baya duk da cewar an zaɓo ɗan cikinsu tare da bashi muƙami a fadar shugaban ƙasa.

 

Yarima Sulaiman Ibrahim shugaban ƙungiyar na arewa, shi ne ya bayyana haka yayin ganawa da Matashiya TV yau Laraba.

 

Abba Isah shi ne mashawacin shugaban ƙasa a kan masu buƙata ta musamman wanda aka zaɓo daga jihar Yobe.

 

Ya ce dun da an zaɓo ɗan cikinsu kuma aka masa mashawarcin shugaban ƙsa kan masu buƙata ta musamman, bay a yin abinda ya kamata.

 

Y ace maimakon ya mayar da hankali wajen samar da ayyukan yi ga masu buƙata ta musamman, sai ya fi karkata wajen raba abinda bai kai ya kawo ba.

 

A sakamakon haka y ace ba za su lamunta ba domin a wannan lokaci ana samun ƙaruwar mabarata daga cikinsu maimakon raguwarsu.

 

A don haka su ka yi koka domin a cewarsu, ba ya yin abinda ya kamata wajen sauke nauyin da ke wuyansa.

 

Za ku samu cikakkiyar tattaunawar a shafukanmu na YouTube da Facebook.

 

 

 

 

Continue Reading

Labarai

Rundunar Sojojin Najeriya Ta Tarwatsa Sansanin Yan Boko Haram Da ISWAP

Published

on

Rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar gano wani sansanin mayaƙa Boko Haram da ISWAP a dajin sambisa tare da lalatashi sannan su ka ƙwato makamai.

 

A wata sanarwa da rundunar ta sanar a shafinta na X wanda aka fi sani da Twitter a baya, rundunar ta ce sun tarwatsa sansanin mayaƙan sannan sun lalata wasu makamai tare da ƙato wasu.

 

An kai harin ne Ngumne, Kawaran, Mangu duka a dazukan Sambisa da Tinbuktu a jihar Borno.

 

Rundunar ta yi amfani da makamai masu hatsari wajen tarwatsa sansanin sannan an ƙato manyan bindigu da hasashi da wasu makamai.

 

Ta ce hakan na daga cikin ayyukan da ta ke yin a kawar da dukkanin ayyukan ta’addanci da ake aikatawa a jihar.

 

Jihar Borno na fama da rikicin mayaƙan ISWAP da Boko Haram fiye da shekaru 10 da su ka gabata.

 

 

 

 

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: