Gwamnan jihar Kano ya yabawa mutanen Kano a bisa ƙin karbar tsarin zanga zangar END SARS da ta haifar da tarzoma a jihohi da dama.

Hakan na ƙunshe cikin sanarwar da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Kano Mallam Abba Anwar ya fitar, ya ce gwamnan ya yabawa shugabannin addinin musulunci, sarakunan gargajiya na ƙabilu daban daban, da ƙungiyoyin matasa bisa ƙin karɓar tsarin.
Gwamna Ganduje ya ce jami an tsaro sun taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar Kano, sai kuma ƴan jarida da suke ƙoƙarin kawo labarai na gaskiya don isarwa jama a halin da ake ciki.

Gwamna ganduje ya ce jihar Kano gari ne na zaman lafiya kuma zai cigaba da zama lafiya musammman idan al umma suka bada hadin kai, kamar yadda ya ce, aikin tsaro ya shafi kowa da kowa.
