Babban sakataren yaɗa labaran mai girma gwamnan Kano Mallam Abba Anwar ya ce zuwan Mujallar Matashiya ya sanya tsofaffin ƴan jarida sun duƙufa wajen dogaro da kansu ta hanyar buɗe jaridu na yanar gizo.

Abba Anwarya bayyana hakane a yayin da yake jawabi a wajen bikin cikar Mujallar Matashiya shekaru huɗu da kafuwa.
Ya ce jajircewar shugaban Mujallar Matashiya ya nunawa duniya cewar duk abinda mutum ya sa a gaba zai kai ga nasara a kansa.

“Lokacin da Abubakar ya fara mujallar Matashiya ta takarda, ba zan iya tunawa ba, amma bana tsammanin a cikin abokanmu da suke aikin jarida babu wanda ya zo da wata online news papper sai bayan da Abubakar ya fara sannan zuka zabura hakan ya zamto matashiya ga sauran ƴan jarida.” Inji Mallam Abba Anwar.

Cikin jawabinsa Abba Anwar ya bayyana mujallar Matashiya a matsayin kafar yaɗa labaran da ke saka labarai na gaskiya ba tare da cin zarafin al’umma ba.
Ya bada misali da irin alaƙar Mujallar Matashiya da ofishin ƴan sanda a Kano, wanda ya ce hakan ya tabbatar da cewar wajibi ne a gamsu da irin yadda ake gudanar da aiki a ciki.
Ya ƙara da cewa abin a yaba ne musamman yadda mujallar Matashiya ta zama sansani na horas da matasa sana’o’i kyauta, wanda babu wata kafar yaɗa labarai da ke yin hakan.
Abba Anwar ya yi godiya ga mutanen da ke ƙarfafawa shugaban mujallar Matashiya gwiwa musamman Muhammadu Aminu Adamu Abba Boss, wanda ya zamto yana tallata abubuwansa a mujallar don ƙarfafar ma aikatan.
Sannan ya ce ayyukan da ake gabatarwa a ciki musamman labarai na ƙasa ƙasa da shirye shiryen da ake gabatarwa, ya nuna kwarewa ta aiki tare da jajircewa a kan aiki.
An yi taron ne a ranar Asabar ɗin da ta gabata kuma a yayin taron ne aka bada kyautuka ga mutanen da suka samu nasara a gasar shirin Ƴar Cikin Gida wanda aka tattauna da Mallam Abba Anwar.
Mutane biyar ne suka samu kyautuka kamar
1 Mubarak Aminu – Shadda yadi biyar da kuɗi naira dubu biyu.
2 Aminu Tukur – Shadda yadi biyar da kuɗi naira dubu ɗaya
3 Sulaiman Aminu Sule – Shadda yadi biyar
Maryam M Abdullahi Kaduna – Kuɗin kati dubu ɗaya.
5 Aliyu Adamu – Kuɗin kati naira dubu ɗaya.