Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Mujallar Matashiya ta karrama mutane 13

Mujallar Matashiya ta zaɓo wasu daga cikin muhimman mutanen da suke bata gudunmawa tare da karramasu.

1, An karrama kwamishinan ƴan sandan jihar Kano Habu A. Sani a bisa yadda ya jagoranci bada horon sana o i kyauta wanda rundunar yan sanda ta kasa ke yi tare da jajircewarsa a kan aiki wajen ganin an kawar da muggan ayyuka a jihar Kano

DCP Balarabe Sule ƙofar na isa ne ya wakilci kwamishinan ƴan sandan jihar Kano a yayin taron.

2, Matashiya ta karrama kakakin ƴan sanda na jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa a bisa kyakkyawar alaƙar aiki mai ƙarfi da mujallar Matashiya don wayar da kan al umma wajen wanzar da zaman lafiya.

3, An karrama shugaba rukunin gidajen gonar Nana Farms Limited Alhaji Muhammadu Aminu Adamu Abba Boss, a bisa gudunmawar da yake bawa mujallar ta hanyar zaɓarta a matsayin hanyar tallata hajarsa.

4, An karrama Hajiya Asma’u Saddiƙ a bisa kyakkyawar alaƙar aiki wajen yaɗa shirye shirye da za su amfanar da al umma, tare da hanyar samawa matasan da aka koyawa sana a a mujallar Matashiya jari.

5, Mujallar amatashiya ta karrama Dakta Ashir T. Inuwa a bisa gudunmawarsa ta hanyar bada lokaci da shawarwari don inganta ayyukan mujallar.

6, Mujallar Matashiya ta karrama Dakta Zahra u Muhammad Umar bisa gudunmawarta wajen shirye shirye a kan aure don inganta zamantakewar aure a tsakanin ma aurata.

7, Haka kuma an karrama Malama Fatima Nabulisi Baƙo Malama Tasalla dalilin shirin da ake gabatarwa na Ma aurata tare da bada magunguna don kare lafiyar al umma

8, An karrama Mallam Muhammad Tukur Moriki don shirin ilmantarwa a bisa addinin musulunci.

9, Sai Mallam Isah Abdullahi malamin shugaban mujallar Matashiya a lokacin yana makarantar firamare.

10, Sai Usman Tijjani Abdulkadir wanda ke kokarin wajen shirye shiryen don sanar da mujallar ga Al umma.

11, Aminu Garba Indabawa kuwa an karramashi bisa damar alakar aiki tsakanin gidan Rediyon Aminci da Mujallar Matashiya

12, sai Aminu Idris daga Arewa Radio wanda yayi ƙokarin samar da lokaci don shirye shirye a kan mujallar Matashiya.

13, Abubakar Bala Lawan Baban Xee ASP kuwa mawaki ne da ya waƙe mujallar Matashiya a yayin bikin cikar mujallar shekaru huɗu da kafuwa

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: