Tsohon kwamishinan ayyuka da raya ƙasa na jihar Kano Injiniya Mu’az Magaji Ɗan Sarauniya ya bayyana cewar da kansa ya buƙaci gwamnan Kano Ganduje ya cireshi a matsayin kwamishina.

Ɗan sarauniya ya bayyana hakan ne a cikin shirin ciki da gaskiya wanda ake gabatarwaa Mujallar Matashiya.

Ya ce kalaman dayayi lokacin rasuwar Mallam Abba Kyari, rashin fahimta ne ya shiga ciki har fadar shugaban ƙasa ta nuna fushi a kai.

Sakamakon kada alaƙar fadar shugabanƙasa da gwamnan Kano Ganduje ne ya sa ya buƙaci a saukeshi daga kwamishina don ɗorewar zumuncinsu.

Kalmar WIN WIN dai ita ta jawo cece kuce a wancen lokaci kuma ya ce dalilin faɗarta shine”Lokacin da Mallam Abba Kyari ya mutu  ya mutu ne a yayin annoba, kuma duk wanda ya mutu lokacin annoba ana sa masa rai da rahama, WIN ta farko kenan, Mutanen Najeriya na kokawa da ogfishin Abba Kyari to yanzu ya mutu an smau damar da za a yiwa ofishin gyara, WIN ta biyu kenan ” a cewar ɗan Sarauniya.

Za ku iya kallon cikakken shirin yau Lahadi a shafinmu na YOUTUBE da ƙarfe 7 na yamma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: