Wasu da ake zargi mayan kungiyar Boko Haram ne sun kashe mutane goma sha biyu a ƙauyen Takulasi kusa da garin Chibok a jihar Borno.

Wani mazaunin garin y ace mayakan sun shiga ƙauyen a motoci ɗauke da bindigogi kuma suka kasha mutane goma ƴan garin sai mutum biyu ƴan sintiri masu taimakawa jami an tsaro wajen yaki da Boko Haram.
Wannan ne hari na baya bayan nan tun lokacin da aka raba gari tsakanin kungiyar Boko Haram da ISWAP.

Sai dai har yanzu hukumomi bas u ce komai a dangane da harin da aka kai ba.
