cibiyar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an amu ƙarin mutane 155 masu ɗauke da cutar a faɗin ƙasar.

Cikin jihohin da aka samu jihar Legas ce ke kan gaba da mutane 85.
Ko da jiya Talata sai da kwamishinan Lafiya na jihar Legas yaa bayyana cewar akwai yuwuwar sake saka dokar kulle sakamakon samun yaɗuwar cutar.

Shugaban kwamitin yaƙi da cutar wanda fadar shugaban ƙasa ta kafa Boss Mustapha ya ce cutar na cigaba da ƙaruwa ne sakamakon mutanen da ke dawowa daga ƙasashen ƙetare ba tare da sun je an musu gwajin cutar ba.

Wannan ke nuni da cewar nan da makwanni biyu masu zuwa cutar ka iya yaɗuwa sosai a sassa daban daban na faɗin Najeriya.