Fitaccen mai kama ƴan fashi da makami a Najeriya Alhaji Ali Kwara ya rasu a yau Juma’a.

Ali Kwara ya rasu a Abuja bayan ya sha fama da jinya.
Ya rasu ya bar mata ɗaya da ƴaƴa huɗu.

An haifi Ali Kwara a Azare da ke karamar hukumar Katagun jihar Bauchi.

Kafin rasuwarsa, mutum ne da ke kama ƴan fashi da ɓarayi, kuma yayi nasarar kama manyan ƴan ta’adda masu tarin yawa.