Wasu yan bindiga sunyin awon gaba da iyalan shugaban majalisar dokokin jihar Adamawa Aminu Iya Abbas  guda biyu.

Haka kuma yan bindigar sun kashe  yan bijilanti biyu a wani hari da suka kai gidan  shugaban  majalisar  dokokin jihar.

Rundunar yan sandan jihar ta bakin kakakin rundunar Sulaiman Nguroje ya tabbatar  da faruwar lamarin ,yayin da yace tuni kwamishinan yan sandan jihar ya bayar da umarnin bincike akan lamarin don kubutar da iyalan shugaban majalisar  da akayi awon gaba da su

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: