Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya reshen jihar Kano ta kama mutane 92 da ake zargi da safarar kayan maye.

Hukumar ta bayyana cewar ta kama mutanen ne a watan da ya gabata, sannan ta kwace kwayar da ta kai nauyin kilogram 987.024.

Kwamandan hukumar a jihar Kano Dakta Ibrahim Abdul y ace wasu daga ciki an sallamesu bayan kwararru a hukumar sun shiga tsakani don wayar da kansu a kan illar kayan maye.

Kwamandan hukumar y ace ana samun nasara wajen dakile ayyukan mutanen da suke safarar kayan maye a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: