Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta jaddada sake bada dama don yin rijistar katin zaɓe a watanni ukun farko na shekarar 2021 mai kamawa.

Shugaban hukumar na riko Air Vice Marshal Ahmed Muazu mai ritaya ne ya bayyana hakan a yayin wani zama da shugabannin jam iyyu a helkwatar hukumar da ke Abuja.

Ahmed Muazu ya buƙaci shugabannin jam iyyun da su yi kira da mabiyansu wajen bin dukkan matakan kariya daga kamuwa da cutar Korona a yayin yin rijistar.

Sannan hukumar ta yabawa jam iyyun ganin yadda aka gudanar da zaben gwamnonin Edo, da Ondo ba tare da samun hayaniya ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: