Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Wani mutum ya hallaka bazawarin tsohuwar matarsa

Rundunar yan sandan jihar Jigawa ta ce ta baza jami anta don kamo wani mai suna Umar da ake zargi ya cakawa saurayin tsohuwar matarsa wuƙa har ya rasa ransa.

Mai Magana da yawun ƴan sanda a jihar SP Abdul Jinjiri yace lamarin ya faru a ranar Litinin din da ta gabata a ƙauyen Dakaiyawa ƙaramar hukumar Kaunagama a jihar.

Ya ce sun samu ƙorafin Umar da kashe wani mai suna Sale Dange mai shekaru 45 ta hanyar caka masa wuƙa a cikii.

Rahotanni sun nuna cewar marigayin suna soyayya ne da tsohuwar matar Umar wanda tuni suka rabu.

SP Abdu Jinjiri y ace jami ansu sun ɗauki mutumin zuwa asibiti kuma a nan ne aka tabbatar ya rasu.

Ya ƙara da cewa tuni aka bada umarnin kamo wanda ake zargin tare da cigaba da bincike a kan ƙorafin.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: