Gwamnatin jihar Kano za ta shirya tsarin mayar da ƙananan yara da almajirai gaban iyayensu.

Kwamishiniyar harkokin mata a jihar Kano Dakta Zahra u Muhammad Umar ce ta bayyanawa Mujallar Matashiya hakan a yayin zantawa da ita a bisa cigaban da aka samu a ma aikatar tsawon shekara ɗaya.

Dakta Zahra u ta ce za su zauna da al ummar jihar Kano masu hannu da shuni don ganin an tallafawa iyayen yaran.

Ta kara da cewa gwamnatin jihar ta samar da cigaba mai yawa a ma aikatarta kamar, tallafawa mata da kayan aure, biyan kuɗaɗen haya ga gajiyayyu, sannan sun magance dukkan matsalolin da suke damun gidan renon yara a Kano.

Haka kuma ta bayyana cewar gwamnan Kano ya ginawa ma aikatarta cibiyar lura da masu taɓin kwakwalwa a sanaɗin shaye shaye kuma babban cigaba ne ga al ummar jihar Kano.

Leave a Reply

%d bloggers like this: