Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Ya kamata gwamnati ta sassautawa talakawa – Ɗan Larabawa

 

Shugaban Gidauniyar Tallafawa Mabukata daga tushe Grassroot Care and Aid Foundation GCAF Ambasada Auwal Muhammad Danlarabawa yayi Kira da a duba halin da ake ciki a wannan lokacin na matsi da durkushewar hada hadar samu Wanda hakan ya faru sakamakon annobar cutar Korona.

Ambasada Auwal Danlarabawa yace gwamnatin Tarayya data jihohi ya kamata su zauna su duba halin da ake ciki da gaggawa Dan ganin an samawa talaka sauki maimakon Kara jefashi cikin kunci Wanda zai Kara hasala jamaa a daidai lokacin da ake fafitukar farfadowa Daga yanayin da ake fama dashi.

Kara kudin man fetur din Nan ba karamin tashin hankali bane sannan zai saka a sake samun hauhawar farashin kayayyakin anfanin yau da kullum Wanda dama tuni sun Kai matakin da ake kokawa da tsadar da sukayi ga rashin kudi da kwanciyar hankali.

Danlarabawa ya Kara da cewar rashin tsaro da tabarbarewar rayuwa yasa da yawa an fara tunanin gwara mutuwa ma da wannan rayuwar da ake ciki musanman a yankunan da ake fama da matsalolin rashin tabbacin tsaro.

Al’ummar da take cikin wannan yanayi tana bukatar lallashi da Samar da hanyoyin tsausasawa kwarai da gaske Kar akai mutane bango duba ga yadda ake kukan cewar agajin da ake fada baya kaiwa ga Mabukata da ya kamata su samu wannan agaji.

A karshen Amb Auwal Danlarabawa yayi Kira ga gwamnonin arewa da su saurari al’ummar su don jin bukatun da suke addabarsu kuma a magancesu a lokacin da ya kamata Kar a samu akasin da ba za’a iya magance shi ba.

Amb Auwalu Muhd Danlarabawa
Shugaban Gidauniyar Tallafawa Mabukata Daga Tushe wato GRASSROOT CARE & AID FOUNDATION ( GCAF )

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: