Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta yi nasarar cafke wani mai suna Habibu Saleh Cikawa da ke ƙaramar hukumar gabasawa, bisa zargin garkuwa da wata yarinya ƴan shekaru takwas.

Yayin da aka yi holen mai laifin a farfajiyar rundunar da ke unguwar Bompai a yau, Habibu Saleh mai kimanin shekaru 24 ya bayyanawa Mujallar Matashiya cewar shi ya yi garkuwa da yarinyar kuma ya nemi kuɗin fansa naira miliyan goma daga bisani aka daidaita a kan naira dubu ɗari biyar.

Ya ce yarinyar ta mutu  a wajensa kuma ya binneta da kansa.

Matashin ya ce ya kashe kuɗin ne ta hanyar caca da neman mata da kuma shaye shaye.

Kakakin yan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Kiyawa ya ce jami ansu na kan kace kwabo ne suka kamo matashin har tsawon wata shida, kuma sun bibiyi ƙorafin har zuwa jihohin Kaduna, da Legas.

A yanzu haka sun kama matashin kuma sun tabbatar da cewar yarinyar ta mutu tsawon watanni shida.

Mahaifin yarinyar ya buƙaci hukumar ƴan sanda da su tsananta bincike a kan lamarin don gano sauran mutanen da ke da hannu a ciki.

Mai magana da yawun ƴan sandan Kando DSP Abdullahi Kiyawa ya ce za su cigaba da bincike tare da gurfanar da duk wanda suka samu da laifi a gaban kotu don girbar abinda ya shuka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: