Majalisar ɗinkin duniya ta bayyana cewa an samu rahoton masu aikata fyaɗe guda 3,600 a yayin dokar zaman gida a Najeriya.

A yayin da take jawabi, mataimakiyar sakataren majalisar Amina Muhammed ta bayyana takaicinta a bisa yadda ake cin zarafin mata a Najeriya.
Ta bayyana hakan ne a yayin taron ƙarawa juna sani kan cin zarafin mata da ƙananan yara a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja.

Amina Mumammad ta ce a dukkanin jihohin Najeriya an aikata laifin fyaɗe fiye da guda 100.

Ta ce ofishinta zai cigaba da aiki da ma aikatar mata a da ke Najeriya don kawo ƙarshen lamarin.