Daga Yahaya Bala Fagge
Shahararren dan ta addan nan daya addabi kasashen yammacin afirika ibrahim shekau ya saki wani sabon faifan bidiyo da yake caccakar shugaban hafsin sojojin nigeria Janar Tukur Burtai cewa, ya gagara a kamashi saboda aikin allah yake yi.
A cikin bidiyon mai tsawon mintuna 30 yace, ba za a iya kamashi ba domin allah ne yake kareshi.
Rundunar sojin nigeria dai ta dade tana cewa ta kashe shekau, amma a lokuta da dama akan ji shugaban na boko haram na yin maganganunsa da kuma kai hare-hare.