Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Bayan ya hallaka budurwarsa, daga ƙarshe kotu ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya

Babbar kotun jihar Ogun ta yankewa wani mai suna Musiliu Owolabi da ake tuhumarsa da hallaka masoyiyarsa.

Lamarin ya faru aranar 12 ga watan Nuwamban shekarar 2019.

Mai gabatar da ƙara ya bayyanawa kotu cewar, matashin ya ɗauki budurwarsa mai suna Afusat zuwa wani Otel, kuma a nan yayi sanadiyyar rayuwarta, sannan ya ɗauketa ya binneta a cikin wani kango.

Alƙalin kotun Mosunmola Dipeolu ya ce laifin ya ci karo da sashe na 319 na kundin manyan laifuka na jihar Ogun.

Daga ƙarshe dai an yankewa Musiliu hukuncin kisa ta hanyar rataya.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: