Yan bindigaYan bindiga

Abubakar Murtala Ibrahim

Kasuwar ƴan bindiga na cigaba da tumbatsa a Arewa, baya ga mutanen da ake sacewa ana hallaka wasu a kullum.

Kusan makwanni biyu kenan ana fuskantar hare haren ƴan bindiga a mabambantan wurare.

Mafi tada hankali anin yadda ƴan bindigan ke kaiwa waɗandake da alaƙa da gwamnati ko shugabanni hari.

Wannan ya sakawa mutann da basu da galihu shakku ganin yadda lamarin ke faruwa kamar yadda wasu suka bayyanawa mujallar Matashiya.

A makwan da muka yi bankwana da shi aka sace mutane a jihar Kaduna, ciki har da ɗaliban da ke ke karatu a jami ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

Cikin makonne dai aka kai hari wani gari a Kaduna tare da hallaka hakimi da ɗansa.

Jami an tsaron ma basu tsira ba ganin yadda aka sace wasu ƴan sanda tare da neman kuɗin fansa.

Daga ɓangare na siyasa ma haka lamarin yake wanda a yau aka wayi gari da gawar shugaban jam iyyar APC mai mulki a jihar Nassarawa bayanƴan bindiga sun sacesh.

A ranar juma ar da ta gabata ma sai da aka sace wasu masallata a jihar Zamfara bayan idan da sallar juma a.

Haka zalika daga ɓangaren gwamnati, a karo na uku aka sake kaiwa gwamnan jihar Borno Babagana Zulum hari, ko da yake harin da  ƴan bindiga ke kaiwa a gashin ƙasar ya bambanta da na sauran wurare.

Hanyar Kaduna zuwa Abuja ta zama siraɗi ganin yadda ake awon gaba da mutane sake babu ƙaidi.

Wanene yayi saura?  an sace talaka, an sace mai kuɗi, an sace basarake, an sace jami in tsaro ankaiwa gwamna hari, bama wannan ba, alƙalai ma ba su tsira ba.

Har yanzu ana ta fitar da maƙudan kuɗaɗe da nufin magance matsalar tsaro.

Ta ina za a fara? za ku iya aiko da shawararku ta lamba 08096399266 domin wallafawa

Leave a Reply

%d bloggers like this: