Rundunar yan sandan jihar Naija ta kama wani Abubakar Maidabo a bisa zargin hallaka yayansa guda biyu.
An kama Abubakar mai shekaru 37 a karamar hukumar Magama bayan ya hallaka yayansa cikinsa da adda.
Yayan nasa Umar mai shekaru 8 da Shehu mai shekaru hudu sun rasu, kuma jami an yan sanda sun kamashi a ranar 14 ga watan nuwamban da muke ciki.
Sai dai mahaifin nasu yace ba zai iya tuna wani abu da ya faru ba.
Mai Magana da yawun yan sandan jihar Wasiu Abiodun ya tabbatar da faruwar lamarin kuma yace za su gurfanar da shi a gaban kotu da zarar sun kammala bincike.