Gwamnan jihar Kano ya bada umarni ga hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe ta jihar Kano don bibiya da sa ido wajen biyan kuɗin makarantar ɗaliban jihar Kano da ke karatu a Faransa.

Zunzurutun kuɗin ya kai naira miliyan sittin da bakwai da dubu ɗari biyar da goma sha bakwai da ɗari biyar da ɗari biyar da tamanin da shida N67,517,586.00.

Ɗaliban dai malamai ne a wasu jami’o’in jihar Kano kuma an turasu ƙaro karatu ƙarƙashin yarjejeniyar karatu tsakanin jihar Kano da ƙasar Faransa.

Shugaban hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci da rashawa a jihar Kano Muhuyi Magaji ne zai jagoranci kwamitin da zai sa ido kan yadda za a biya kuɗin.

Ko da a watan Fabrairun shekarar da muke ciki sai da gwamnan ya amince da fitar da kuɗi naira miliyan 100 don biyan kudin makaratar daliban kamar yadda babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Kano Mallam Abba Anwar ya sanar..

Leave a Reply

%d bloggers like this: