Gwamnatin jihar Sokoto ta bayyana dokar ɗaurin rai da rai ga duk wanda aka kama da laifin fyaɗe a jihar.

Gwamnan jijhar Aminu Waziri Tambuwal mne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da sashen cibiyar lura da masu aikata laifukan fyaɗe a jihar.
An ƙaddamar da cibiyar a jiya Laraba wanda aka saka mata sunan ƴar fitaccen malamin addinin islma (Sheik Usman BinFodiyo) Nana Khadija .

Gwamnan ya ce tuni majalisar dokokin jihar ta zartas da dokar cikin kundin dokokin jihar Sokoto.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin kwamishinan shari’a na jihar Sulaiman Usman ya ce bayan dokar akwai tara daga naira dubu hamsin zuwa miliyan ɗaya.