Hen, Chicken eggs and chickens eating food in farm

Ƙungiyar masu kiwon kaji ta ƙasa a Najeriya ta koka a bisa hauhawar farashin kayan abinci a ƙasar.

A yayin taron manema labarai da suka gudanar a yau, shugaban ƙungiyar ya bayyana cewar manoma kaji na cikin tsaka mai wuya.

A sakamkon hauhawar farashin kayan abinci wanda ya yi sanadiyyar tsadar kaji da kwai a faɗin Najeriya.

Ƙungiyar ta bayyana cewar ƙananan masu kiwon kaji sun rasa aikinsu tare da waɗanda k dafa musu a al’amuransu.

Shugaban ƙungiyar Ezekiel Ibrahim MAM ya ce a sakamakon annobar Korona da dokar kulle da aka saka a a Najeriya an samu koma baya wajen samar da kaji masu kwai da waɗanda ake kiwonsu domin nama.

Ƙungiyar ta buƙaci gwamnatin tarayya ta dubu lamarin ganin yadda masara da sauran kayan sarrafa abincin kajin farashinsu ke cigaba da hauhawa a ƙasar.

Ko da a shirin da Mujallar Matashiya ke gabatarwa na Abokin Tafiya da ake tattaunawa da shugaban gidajen gonar Nana Farms Alhaji Aminu Adamu ya yi wannan koke a baya, sakamakon cikas da masu kiwon kajin suka samu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: