Rundunar yan sanda a jihar Ibadan ta kama wata Emila Sunday da ta yi yunkurin siyar da jaririnta dan watanni uku

Emila mai shekaru 21 a duniya ta yi cinikin jaririn nata kan kudi naira dubu dari da hamsin.
Yan sanda sun kamata a ƙauyen Ire a jihar Anambara.

Kakakin hukumar yan sanda a jihar Muhammad Haruna ya tabbatar da faruwar lamarin, wanda y ace an ceto jaririn kuma yana cikin koshin lafiya.

Sannan sun cigaba da zurfaffa bincike a kan wadda ake zargi.