Gwamnan jihar Kano ya sha alwashin kammala aikin titin da ya jama’a suka daɗe suna kuka a kansa wanda ya tashi daga Rimin Gado zuwa Gulu har Jeli.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan yayin da ya je ziiyarar gani da idowajen aikin titin da aka fara kuma ya yi alƙawarin kammalashi batare da ɓata lokaci ba.

Ya ce a baya wani ɗan majalisa ne ya yaudari al’ummar yankin, kuma bai yi kataɓus a kan aikin ba.

Ganduje ya ce za’a gudanar da aikin tare da magudanar ruwa tun daga farkonsa har ƙarshe.

A wasu kalamai na gwamnan da ke nuni da gazawar wakilin yankin a majalisar ƙasa, gwamnan ya caccaki wakilin da cewar ya ya ci taliyar ƙarshe.

A cewar Ganduje, tsawon shekarun da ɗan majalisar ya ɗauka, bai amfanawa yankin da komai ba.

Ganduje ya sha alwashin sharewa jama’ar hawayensu ta hanyar cigaba da gudanar da aikin don su amfana kamar yadda suke buƙata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: