Ƴan sanda a jihar Akwa Ibom sun kama wata Eka Ime bisa zargin hallaka mahaifiyarta.

Al amarin ya faru a ranar juma ar da ta gabata, ta hallakata ta hanyar sassara jikinta.
Wani da lamarin ya faru a kan idonsa ya bayyana cewar, matasa a yankin sun tashi cikin jimami da baƙin cikin abinda ya faru.

Yayinda ƴan sanda suka je kama wadda ake zargi, ta nuna rashin damuwarta a kai, lamarin da ya ƙara bawa mutane mamaki.

Matar ta furta da bakinta cewar bata damu ba don jami an yan sanda sun kamata.
Mai magana da yawun yan sanda a jihar Odiko Macdon ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma y ace za a su binciki kwakwalwar wadda ake zargi domin abin akwai alamar ba a hayyacinta take ba.
A cewarsa, lafiyayyen mutum ba zai iya hallaka mahaifiyarsa da kansa ba.