An yi kira ga mata da su kasance masu koyi da matan manzon Allah cikin zamantakewar aurensu.

Dakta Zahra u Muhammad Umar ce ta bayyana hakan a cikin shirin Zamantakewar Ma aurata da ake gabatarwa a Mujallar Matashiya.

Ta ce kishi da wasu matan key i ya wuce hankali, idan za a yi kishin sai a kalli gidan manzon Allah don a yi koyi da shi.

Ta ƙara da cewa mafi yawan matsalolin da ake samu a tsakanin ma aurata musamman ɓangaren kishi, barin turbar addinin musulunci ne ya haddasa hakan.

Sannan ta roki iyaye da suyi riƙo da al adu masu kyau don ƙara danƙon soyayya tare da ɗorewar zaman auren ƴaƴansu.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: