Rundunar ƴan sanda a Katsina ta Kama wata mai suna Zainab Adamu bisa siyar da jinjirinta naira dubu ɗari uku 300,000.

Zainab da aka fi sani da Justina da ke sana’ar Karuwanci ta cefanar da jinjirin nata ɗan watanni huɗu ga wani da ke jihar Anambara.
Jami an yan sanda a Katsina sun kamata a Ƙofar Ƙaura da ke Katsina bayan aamun bayanan sirri a kan lamarin.

Tuni aka cafke wasu ƴan ƙabilar Igbo da aka haɗa kai da su da waɗanda suka siyi jinjirin.

Mutann da aka kama wasu ƴan jihar Anambra ne wasu kuwaa ƴan jihar Delta ne.
Mai magana da yawun ƴan sanda SP Gambo Isah ya ce an kamasu a ranar 26 ga watan da ya gabata ne kuma ana cigaba da gudanar da bincike a kansu.