Shugaban ƙungiyar Boko Haram Abubakar sheƙau yace su suka yiwa mutane yankan rago a Zabarmari da ke ƙaramar hukumar Jere a jiha Borno.

A wani faifan Bidiyo da ya fita na ƙasa da mintuna huɗu, sheƙau ya bayana dalilin da yasa suka hallaka mutanem yankin.

Ya ce mutanen yankin sun kama ɗan ƙungiyar Boko Haram suka miƙawa sojoji wannan ne dalilin da ya sa suka yi musu hakan.

Ya ƙara da cewa duk wanda ya kuskura ya yi makamancin hakan to zai fuskanci irin matakin a suka ɗauka a kan manoman.

Leave a Reply

%d bloggers like this: