Hukumar kare fararen hula a Najeriya NSCDC reshen jihar Ondo ta kama wani mutum mai shekaru 50 bisa zargin yiwa wasu yara biyu fyade.

Kwamandan hukumar Eweka Edenabu ne ya bayyana hakan a Akure, ya ce an kama mutumin ne a ranar 29 ga watan da ya gabata.

Ya ce mutumin ya aikata laifin fyade ga wata mai shekaru 10, bayan sun zurfafa bincike suka gano a makwannin baya ma ya aikata makamancin hakan a kan wata mai shekaru 8 a duniya.

Tuni aka mika yaran da yayiwa aika aika zuwa asibiti don duba lafiyarsu.

Kwamandan y ace ya yaudari yaran ne ya kaisu wani kango kuma a nan yayi aika aikan.

Ya kara da cewa za su gurfanar da su a gaban kotu da zarar sun kammala bincike a kan lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: