Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci tawagar wakilai a ɓangaren al’umma daban daban don ziyarar ta’aziyya jihar Borno.

Sun kai ziyarar ta’aziyya ne fadar gwamna jihar Babagana Umara Zulum a fadar gwamnatin jihar a bisa harin da aka kaiwa wasu manoma da ke yankin Zambarmari a jihar.

Gwamna Ganduje ya jagoranci ɓangaren majalisar zartarwa a gwamnatinsa, manyan malaman addini da sauran jagorori a ɓangare daban daban.

Ya ce sun kai ta’aziyyar ne don jajantawa tare da ƙara ƙarfin gwiwar bada agaji ta fuska daban daban, a cewarsa gwamnatin Kano na iya ƙoƙarinta wajen ganin ta tallafawa marayun da suka rasa iyayensu a sanadin rikicin kuma koda a yanzu akwai waɗanda suke a jihar ƙarƙashinnkulawar gwamnatin.

A yayin ta’aziyyar Ganduje ya miƙa takardar jaje a madadin al’ummar jihar Kano a bisa ibtila’in da ya faru.

Cikin sanarwar da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Kano Mallam Abba Anwar ya fitar ya zayyano wasu daga cikin waɗanda suka bi tawagar gwamnan, ciki har da shugaban majalisar dokokin jihar Kano Abdullahi Gafasa.

A ziyarar makammanciyar wannan, Ganduje ya jagoranci tawagar zuwa fadar Shehun Borno don yi masa ta’aziyya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: