Labarai
Kotu ta tabbatar da hukuncin rataya a kan Maryam Sanda, wacce dama take da ita a gaba?
Bayan ɗaukaka ƙara kan hukuncin da aka yanke mata a wata kotu a Abuja, Babban kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan Maryam Sanda.
An samu Maryam Sanda da hallaka mijinta Bilyaminu Bello.
Tun a shekarar 2017 aka gurfanar da Maryam Sanda a gaban kotu, kuma a shekarar 2020 aka yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya kuma daga bisani ta ɗaukaka ƙara.
Alƙalin da ya jagoranci alƙalai uku a kan shari’ar Steven Adah ya ce kotuna da ikon yin adalci amma ba bisa son zuciya ba.
An samuMaryam Sanda da hallaka mijinta da wuƙa kamar yadda aka samu shaidu a kotu suka tabbatar.
Shin Maryam Sanda na da wata a nan gaba?
Na san mai karatu zai so ya san halin da ake ciki, a nan gaba mafitar da za ta iya kuɓutar da Maryam Sanda bai wuce shigowar ƙungiyoyin duniya kamar ƙungiyar amnesty ba.
Koda yake akwai damar ɗaukaka ƙara zuwa kotun ƙoli wanda tuni lauyoyinta suka gudanar.
Haka kuma shugabanni na iya yin afuwa ga wanda yayi laifi ko da an tabbatar da laifinsa kuma an masa hukunci a kansa.
Misali gwamna ko shugaban ƙasa na da damar da zai iya yafewa wanda aka samu da laifi matuƙar hakan bai ci karo da doka ba.
Waɗannan sune hanyoyin da Maryam Sanda za ta iya samun tsira daga hukuncin da aka yanke mata a kotu.
Labarai
Tinubu Ba Zai Sauka Daga Manufofin Da Ya Ke Kai Ba – APC
Jam’iyyar APC a Najeriya ta ce shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ba zai jingine kudirin da ya dauka na gyaran kasa tare da komawa baya ba.
A cewar jam’iyyar matakin da shugaban ke ɗauka hanya ce don kawo sauyi da cigaba ga ƙasar.
Sannan jam’iyyar ta musanta zargin yin magudi a yayin zaben da aka yi a Jihar Edo.
A sakon da jam’iyyar APC ta fitar a yau wnda ke zama martani ga jam’iyyar PDP, daraktan yada labarai na jam’iyyar Alhaji Bala Ibrahim ya ce jam’iyyar ba ta da nufin sauka daga turbar demokaradiyya.
Ya ce tsari da manufofin da jam’iyyar ta saka a gaba asara ce kuma ci gaba ne ga ƙasar.
Haka kuma tsarin da su ke kai ba zai tauye demokaradiyya ba.
Labarai
Kotu A Ekiti Ta Yanke Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Masu Aikata Fashi Da Makami
Babbar kotu a jihar Ekiti ta yanke hukuncin kan wasu mutane uku da ake samu da aikata fashi da makami.
Kotun a jiya Laraba ta yankewa mutanen hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Wadanda aka samu da laifin sun hada da Alexander Solomon , da Desmond Peter sai Eric Tile.
Kotun ta sallami cikon na hudun da aka zarga Promisr Shir bayan da aka gani ba shi da hannu a ciki
Wadanda aka yankewa hukuncin an samesu ne da laifukan fashi da makami, mallakar makaami ba bisa kaida ba da kuma kisan kai.
Wanda da aka yankewa hukuncin sun aikata laifin ne a ranar 7 ga watan Yulin shekarar 2022 a tsakanin Illumoba-Aisegba da ke kan titin Ekiti zuwa Aisepba Ekiti.
A wajen ne kuma su ka yi fashin naura mai kwakwalwa ta tafi da gisanka, da kudi naira 540,000 wayoyin hannu da sauransu.
Saannan su ka yi kisan kai
Bayan gabatarwa da kotun hujjoji ne kuma kotun ta gamsu tare da yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya
Labarai
Majalisar Dattawa Na Shirin Yiwa Kundin Tsarin Mulkin Kasar Kwaskwarima
Majalisa dokoki a Najeriya na shirin yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima bayan da kotun koli ta bai wa kananan hukumomi yancin gashin kansu.
Majalisar ta ce za ta yi gyaran ne don sake jaddada hukuncin kotun koli da ta bai wa kananan hukumomin dama.
Kudirin ya fito daga mataimakin shugaban majalisar Barau I Jibril kumaa ya samu goyon bayan Sanata Abdul Ningi fa Sanata Tahir Monguno.
Daga cikin hukuncin da kotun ta yi ta umarci a tura kason kananan hukumomin kai tsaye zuwa asusunsun, maimakon hadaka da asusun jiha da ake yi a baya.
Shugaban majalisar Godswill Akpabio ya jaddada cewar, majalisar na goyon bayan hukuncin da kotun kolin ta yi, ya ce za su yi aiki a kundin tsarin mulkin domin ganin an shigar da dokar a ciki.
A ranar 11 ga watan Agusta ne dai kotun koli a Najeriya ta yanke hukunci damgane da bai waa kananan hukumomi yancin gashin kansu.
Wanda kotun ta ce daga lokacin gwamnatin tarayyaa ta dinga aike da kudadensu kai tsaye ga asusunsu.
-
Labarai8 months ago
Mafi Karancin Sadaki A Najeriya Ya Koma Dubu 99,241
-
Mu shaƙata2 years ago
Kun San Ma’anar Kalmar Chiza Dani? Waƙar Da Ke Tashe A Kwanakin Nan?
-
Labaran ƙetare5 years ago
Wajibi ne duk wani namiji ya Auri mata Biyar ko a ɗaure shi a gidan yari— Sarkin Swaziland
-
Al'ada5 years ago
Fahimta ta a kan matsalar aure a ƙasar Hausa
-
Labarai5 years ago
Ba kwaya ƴan sandan kano suka kama ba, babu sinadarin maye a cikin maganin – NAFDAC
-
Addini4 years ago
Lokutan da ake saurin karɓar addu’a
-
Lafiya6 years ago
Menene Genotype ? Amfanin yinsa kafin Aure – Mujallar Matashiya
-
Mata adon gari5 years ago
Sinadarin gyaran gashi – Adon Gari