Ƙungiyar malaman jami’a a Najeriya ASUU ta ce babu ranar komawa bakin aiki. har sai an sakar musu kuɗaɗensu.
Ƙungiyar ta ce ba zata koma bakin aiki ba sai an biyasu albashinsu.
A halin yanzu ƙungiyar na tattaunawa da mambobinta kan sabon tayin da gwamnatin tarayya ta yi musu a watan da ya gabata.
Tun watanni takwas da suka gabata ƙungiyar ta fara yajin aikin a bisa ƙin biya musu buƙata da gwamnatin tarayya ta ƙi yi.
Cikin buƙatun akwai biyan albashin da aka riƙe musu da alawu, sai dai an cimma wasu daga ciki.