Majalisar wakilai a Najeriya ta yi watsi da buƙatar tsige shugaban ƙasar Muhammadu Buhari.

Wani ɗan majalisa a jihar Rivers Kingsley Chinda ne ya nemi ƴan najeriya su tilastawa wakilansu don tsige shugaban daga mulki.
Sai dai majalisar ta ce hakan ra’ayi ne na mutum guda kuma adawa ce ta siyasa.

Cikin wata sanarwar da mai Magana da yawun majalisar wakilai Benjamin Kalu yace babu wata hujja ko dalili tunda shugaban bai halarci majalisa an bashi shawara yaki amfani da ita ba.

Majalisar ta buƙaci shugaba Buhari ya bayyana a gabanta a bisa kisan manoma sama da 40 a jihar Borno.
Shugaban ya amsa tare da amincewa bayyana a gaban majalisar don amsa tambayoyi a kan al amuran da suka shafi tsaro a Najeriya
Hankulin ƴan Najeriya da wasu ƙasashen ya tashi a bisa kisan manoma a Borno ta hanyar yankan rago, wanda ƙungiyar boko haram ta ɗauki nauyin harin kamar yadda shugaban ƙungiyar Abubakar Shekau ya bayyana cikin wani faifan bidiyo.