Mujallar Matashiya ta gudanar da bita ga kafafen yaɗa labarai daban-daban waɗanda suke wallafa labarai cikin harshen Hausa a kafafen sadarwar zamani.

An gudanar da bitar don shawo kan ƙalubalen da aikin jarida ke fuskanta wajen rubutu da dokokin aikin jarida.

Malamai da dama ne suka gabatar da maƙala, guda daga cikinsu akwai Dakta Muhammad Sulaiman daga sashen nazarin harshe a jami’ar Bayero a Kano, sai Dakta Ashir T. Inuwa malami a tsangayar nazarin aikin jarida a jami’ar Bayero da ke Kano.

A yayin bitar an maida hankali wajen ƙai’idojin rubutun Hausa, da dokokin aikin jarida.

Shugaban Mujallar Matashiya Abubakar Murtala Ibrahim ya ce, an zaɓi gayyato kafafen yaɗa labarai na kimiyyar zamani don inganta aikin jarida a faɗin Najeriya.

Wasu daga cikin mutanen da suka halarta sun wakilci jaridu kamar haka, Rariya, Nagartacciya, Sirrinsu Media, Siyasarmu, Kadaura, sai jaridar Mikiya.

Sauran sune Dimukuraɗiyya, Arewa Royal Star TV, Sarauniya News, Alƙibla, Film Magazine, Labarai 24, Kogin Wasanni, Whiteblood Multimedia, da Freedom Radio, Aminci Radio sai wasu daga ma’aikatan Mujallar Matashiya.

Mutanen sun fito daga ɓangare daban daban na jihohin Arewacin Najeriya.

Ko da yake sun bayyana farin cikinsu a dangane da hakan, tare da roƙon sake gudanar da bitar a nan gaba.

An gudanar da bitar ne a yau a ofishin Matashiya da ke Kano.

Leave a Reply

%d bloggers like this: