Daga Yahaya Bala Fagge

Gwamnan jihar katsina Aminu Bello Masari ya bada umarnin rufe dukkanin makarantun kwana na Jihar.

Masari ya bayyana hakanne a safiyar yau Asabar lokacin da yakai ziyara makarantar kimiya ta Ƙanƙara, bayan ya gana da iyaye ,malamai,tare da masu ruwa da tsaki akan lamarin.

Wannan umarnin ya biyo bayan sace daliban makarantar kwana ta GSSS Kara  da Ƙanƙara  a daren Juma’a da misalin karfe 9;40

Sannan Gwamnan ya ba mutanen yankin hakuri, da basu tabbacin cewa za su yi duk mai yiwuwa domin ganin an ceto yaran.

Leave a Reply

%d bloggers like this: