Daga Yahaya Bala Fagge

Ƙungiyar Boko Haram ta ɗauki alhakin sace ɗaliban makarantar GSSS dake Ƙanƙara a Jihar Katsina.
Sanarwan ta fito ne daga bakin shugaban ƙungiyar Abubakar Sheƙau cikin wani sakon murya mai kimanin mintuna 4;30 bayan kwanaki uku da sace ɗaliban

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan da zuwan gwamna masari wurin shugaban ƙasa Mahammadu Buhari Daura domin faɗa masa yadda halin tsaron ɗaliban ya ke ciki.

Sannan Masari ya bayyanawa shugaban cewa an gano inda maharan suke tare da ɗaliban.
Matsalar tsaro dai sai kara taɓarɓarewa ta ke a Najeriya musamman a arewacin ƙasar, inda Jama’a da dama na ganin gazawar shuwagabannine ya sa lamarin yaki ci yaki cinyewa,wasu kuma na ganin laifin mutanen gari ne da ba sa bada bayanan sirri ga jami an tsaro.
A daren Juma’ar da ta gabata ne dai aka sace daliban a makarantar su ta kimiyya da ta ke Kankara da misalin karfe 9;40 ,wanda har yanzu babu wani sahihin adadin daliban da aka sace.