Sannarwa ta ƙarshe daga kwamishinan ilimi na jihar Kano Sanusi Ƙiru ya ce gwamnatin Kano ta bada umarnin rufe dukkanin makarantu a faɗin jihar.

Gwamnatin Kano ta ce za a rufe makarantun nedaga gobe Laraba don gudun yaɗuwar cutar Korona.
Hakan ya biyo bayan umarnin da gwamnatin jihar Jigawa ta bayar na rufe makarantun a yau.

Kafin sanarwa a Jigawa kuwa tuni gwamnan Kaduna Mallam Nasir El’rufai ya bada damar rufe makarantu a Kkaduna.

Matakan da gwamnoni ke ɗauka wani salo ne da suka ce na daga hanyar daƙile yaɗuwar cutar.
A wani ɓangaren kuwa al’amarin taɓarɓarewar tsaro ka iya shafar makarantun ɗaliban, ganin yadda aka yi awon gama da ɗalibai ƴan makaranta kusan guda dubu a jihar Katsina.
Tun tuni gwamnatin Najeriya ta sanar da sake juyowar cutar Korona a karo na biyu.
Kuma tuni aka tabbatar da wasu daga cikin manyan jami’an gwamnati na cewa sun kamu da cutar.
Cutar Korona dai ta kawo sauyi a faɗin duniya musamman yadda ta karyar da tattalin arziƙi a duniya.
Har yanzu al’umma na cikin wani matsi sanadin matakin dokar kulle da aka dauka a zamanin Korona na farko.