Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya bada umarnin buɗe iyakokin ƙasa na  Najeriya guda huɗu.

Iyakokin ƙasar na ƙasa sun haɗa da Maigatari, Illela, Mfun, da Seme.

Sanarwar da mai taimakawa shugaban ƙasa kan kafafen sadarwar zamani Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na tuwita a yammacin yau  laraba.

Tun a shekarar 2019 aka sake bada umarnin rufe iyakokin ƙasar na ƙasa, sakamakon fasa ƙwaurin miyagun ƙwayoyi, makamai da safarar shinkafa ƴar ƙasar waje kamar yadda fadar shugaban ƙasar ta bayyana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: