Rundunar yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da sace ɗalibai 80 a jihar.

Mai magana da yawun yan sandan jihar SP Gambo Isah ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce  ɗaliban ƴan makarantar islamiyya ne kuma ƴan bindigan sun sace su bayan sun dawo daga wajen mauludi.

Lamarin ya faru a ƙauyen Mahuta da ke ƙaramar hukumar Ɗandume a jihar Katsina.

Sai dai jami’an ƴan sanda haɗi da dakarun jami’ai kan kace kwabosun samu nasarar ceto mutanen tare da wasu mutane huɗu da aka yi garkuwa da su a baya.

Gambo Isah ya ce an samu nasarar ceto shanu guda 12 da ƴan bindiga suka sace.

Ya ƙara da cewa jami’an na ci gaba da sa ido don ganin an kama yan bindigan da suka gudu da kuma nemo gawawwakin waɗanda aka kashe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: