A yau litinin Majalisar dattawan Najeriya ta amince da kasafin kudi na shekarar 2021 mai kamawa.

Majalisar ta kammala karatu na uku sannan ta amince da kasafin bayan shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin a watan Oktoba.

Shugaban ya gabatar da sama da naira tiriliyon 13 a matsayin kasafin kudin shekarar 2021.

Majalisar ta bayyana cewar ta kammala bitar kasafin wanda ta amince da ware naira tiriliyan 5.6 don ayyukan yau da kullum. Sannan naira tiriliyan 4.1 don gudanar da manyan ayyuka sai tiriliyan 4.1 a matsayin kudaden da za a tattara don gudanar da manyan ayyuka.

An samu ƙarin biliyan biyar a kan kuɗin da shugaban ƙasar ya gabatar wanda hakan ya sa adadin kasafin ya kai tiriliyan 13.5.

A shekarar da ta gabata shugaban ya gabatar da tiriliyan goma a matsayin kasafin ƙudin shekarar 2020.

Leave a Reply

%d bloggers like this: