Rundunar ƴan sanda a jihar Ogun ta kama wasu mutane biyar da ake zargin su da kashe wata matar aure da kuma wani mai keke napep.

Kakakin rundunar ƴan sanda jihar Abinbola Oyeyemi ne ya bayyana haka, inda ya ce waɗanda ake zargin sun aikata laifin ne tun ranar 1 ga watan october wannan shekarar.
Sannan ya ƙara da cewa matar da aka kashe a lokacin tana kan hanyar zuwa kasuwa ne kuma ta haɗu da bata garin suka kasheta sannan suka gudu.

Kazalika ya ce tun wancen lokacin rundunar ƴan sanda take bibiyar su har sai da aka kama su. Kuma tuni kwamishinan ƴan sanda jihar Edward Ajagun ya bayar da umarnin mayar da su shashen binciken manyan laifuka don faɗaɗa bincike.
