Babban bankin Najeriya CBN ya ce akwai yuwuwar darajar Naira ta sake faɗuwa ƙasa a shekarar 2021 mai kamawa.

Hasashen bankin wanda ya tuntunɓi kamfanoni da ƴan kasuwa sama da dubu ɗaya, bankin Najeriya CBN ya tabbatar da cewar akwai yuwuwar farkonm shekarar 2021 naira za ta fadi.

Ko da a makon da ya gabata darajar naira sai da ta fadi har ta kai dala daya matsayin naira 500, kuma daga bisani ta ke hawa da sauka a tsakanin 460 zuwa sama.

Najeriya ta faɗa matsin tattalin arziƙi mafi tsari a cikin shekaru 36 da suka gabata, kamar yadda rahoton bankin duniya ya bayyana.

Faduwar Naira na haifar da hauhawar farashin kayayyaki musamman waɗanda ake kawosu daga waje kuma ake cikinikinsu da Dala, ko da yake kayayyakin da ake samarwa a Najeriya ma faduwar dalar na shafarsa ta hanayar hauhawar farashinsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: