Ma’aikatar shari’a a ƙasar Saudiyya ta saka dokar hana aurar da mutanen da suke ƙasa da shekaru goma sha takwas.

Ministan shari’a kuma shugaban majalisar alƙalai a ƙasar Sheikh Walid Al-Samaani shi ya sanar da hakan bayan da ƙasar ta amince a kan dokar.
An aike da umarnin hakan ga dukkan kotu a ƙasar don tabbatar da dokar.

Tun tuni ake ta sukar lamarin auren ƙasa da shekaru 18 wanda ake ganin na kawo cikas ga lafiya da rayuwar ƴaƴa mata.
