Rundunar yan sanda a jihar Edo ta gurfanar da wani Chibuke Njokwu bisa zargin cizon budurwarsa a mamanta.
Matashin mai shekaru 25 a duniya ya ciji budurwarsa ne a yayin da suke faɗa a tsakaninsu.
Ɗan sanda mai gabatar da ƙara ya bayyanawa kotu cewar al’amarin ya faru a ranar 24 ga watan Disamban da muke ciki.
Alƙalin kotun ya bayyana cewar laifin ya saɓa da sashe na 335 na kundin dokokin jihar.
Sai dai an bayar da belin wanda ake zargi a kan kuɗi naira dubu hamsin, kuma za a ci gaba da sauraren shari’ar a ranar 26 ga watan janairun mai kamawa.