Wasu da ake zargin mayaƙan ƙungiyar Boko Haram ne sun hallaka mutane bakwai a wani ƙauye da ke ƙaramar hukumar Jere a jihar Borno.

An kashe mutanen a ƙauyen Kayamla da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Jere a jihar Borno.

Wani mai suna Musa Bukar ya bayyana cewar an yi jana izar mutanen a asibitin koyarwa da ke jami ar Maiduguri.

Mutane bakwai da aka kashe mafarauta ne kuma lamarin ya faru ne a a jiya Talata kuma bayan sun kashesu sun ƙona gawar mamatan.

Sai dai har zuwa lokacin da muke kammala wannan labarin ba mu ji daga ɓangaren gwamnatin jihar ba.

Ƙaramar hukumar Jere dai a nan mayaƙan Boko Haram suka yanka manoman shinkafa sama da 100 kamar yadda suka yi iƙirarin haka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: