Aƙalla mutane 7 aka kashe yayin da sojoji da dama suka samu raunI bayan wani hari da ƙungiyar Boko Haram ta kai wani ƙauye a Chibok.

Mayaƙan sun yi tsinkaye ne a wani sansanin sojoji da ke kuda wani ƙauye da ke kusa da garin chibok.
Sojoji shida aka kashe da farar hula guda, sai kuma wasu sojoji da aka jikkata.

Lamarin ya faru da yammacin jiya Lahadi kamar yadda wani ɗan ƙungiyar tsaron sa kai Yohanna Bitrus ya shaida

Bayan kaiwa sojoji harin mayaƙan boko haram sun ƙona gidaje 40 tare da awon gaba da ababen hawa.
Bitrus ya ce akwai buƙatar ƙarin jami an tsaro da basu kayan aiki a yanakin don tsare rayukan al ummar garin.
Ko da a kwannanan ma sai da mayaƙan Boko Haram suka hallaka mutane 100 a Nijar.
Sai dai hare haren ƴan Boko Haram ɗin ya fi munanana a Najeriya kamar yadda suke kai hare haren a kai a kai.